Faransa

Ministan Tsaron kasar Faransa ya isa Nijar kan Faransawa da aka kashe

Ministan tsaron kasar Faransa Alain Jupp lokacin da ya sauka kasar Jamhiriyyar Nijar
Ministan tsaron kasar Faransa Alain Jupp lokacin da ya sauka kasar Jamhiriyyar Nijar Getty Images

Ministan tsaron kasar Faransa Alain Jupp a yanzu haka ya sauka Yamai babban birnin kasar Jamhuriyyar Nijar domin tattaunawa da mahukuntar kasar bayan kisan wasu Faransawa guda biyu da aka yi a kokarin kubutar da su daga hannun kungiyar Al ka’ida da ake zargin ta yi garkuwa dasu.Tuni dai ‘yan sandan kasar Faransa masu yaki da ta’addanci suka isa kasar Jamhuriyyar Nijar domin gudanar da Bincike kan kisan Faransawan.A cewar wani jami’in tsaro du Dimanche, yace daya daga cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa dasu tuni ya kudurta auren wata mata ‘yar kasar Nijar a mako mai zuwa, inda dayan abokinsa ya kai masa ziyara a Yamai domin gudanar da bukin auren.Mai Magana da yawun gwamnatin kasar Nijar yace Jami’an tsaron kasar uku ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da masu garkuwa da mutanen suka kai.