Cote d’ivoire

Sau biyar ana kai wa motoci da ma’aikatan majalisar dinkin duniya hari a Abidjan

Dakarun majalisar dinkin duniya na sintiri a Abdjan
Dakarun majalisar dinkin duniya na sintiri a Abdjan Reuters/Luc Gnago

Sau biyar kenan ana kai wa motoci da ma’aikatan majalisar dinkin duniya hari a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.An raunata wani likita da direban motar asibiti yayin daya daga cikin hare-haren, sannan aka kone motoci biyu, aka lalata wasu uku.Mukaddashin mai mai magana da yawun dakarun majalisar dinkin duniya dake kasar Kenneth Blackman ya shaida wa gidan rediyon Faransa Rfi cewa magoya bayan Laurent Gbagbo kadai ke iya kai irin wadannan hare-haren kuma bisa rakiyar jami’an tsaro.Shi ma dai Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya zargi magoya bayan Laurent Gbagbo.