Niger

Amurika ta janye yan kasar ta masu yin hidimar kasa a kasar Nijar

Jami'an tsaro na sunturi
Jami'an tsaro na sunturi RFI/Julie Vandal

Kasar Amurika ta kwashe ‘yan kasar ta guda 98 masu hidimar kasar a kasar jumhuriyar Nijar.Kasar Amurika ta yi haka ne, sabili da abun da ta kira tabarbarewar lamuren tsaro a cikin kasa. Tun dai lokacin da kungiyar Al’kaida,a yankin yammaci Afrika ta sace ‘yan kasar Franshinan guda 2,da kuma su ka tarda ajalin su a cikin fafatawar da ta wakana, tsakanin ‘yan kungiyar da dakarun kasar Franshi a cikin wani yanki na kasar Mali ,dokacin masu fata da fari,’yan kasashen turai da na yammacin ta, su ka tsamtsamta da kasar ta Nijar.Tun dai cikin shekara ta 1962,shekara 2 kenan bayan samun incin kan kasar ta Nijar ne kasar Amurika ta girka wanan tsari na turo’yan kasar ta,domin yin hidima ga kasar Nijar.