Africa ta kudu

An sallami Mandela daga Asibiti

tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu Nelson Mandela,
tsohon shugaban kasar Africa ta Kudu Nelson Mandela, REUTERS/Mike Hutchings

Likitocin da ke kula da lafiyar tsohon shugaban kasar Africa ta kudu Nelson Mandela, a yau Juma’a sun sallami tsohon shugaban bayan ya yi fama da ciwon Huhu, inda mahukuntar kasar suka ce ya dawo gida cikin koshin lafiya, da dariya da wasa da masu zuwa ban gaisuwa. Tuni dai shugaban kasar Jacob Zuma ya lamunci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu bayan ya fice daga zauren taron tattauna matsalar tattalin arzikin kasashen duniya wanda ake gudanarwa a Davos kasar Swithzerland sanadiyar rashin lafiyar tsohon shugaban.Lokacin da mataimakin shugaban kasar ke ganawa da manema labarai a asibitin Milperk dake birnin Johannesburg inda Mandela ke jinya, Mista Kgalema Motlanthe yace tsohon shugaban ya samu kyakkyawar kulawa hannun kwararrun likitocin kasar.