Uganda

Shugaban Uganda Museveni ya sake lashe zabe

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni Reuters/Thomas Mukoya

Shugaban Kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya lashe zaben shugaban kasar da a ka yi a karshen mako, inda ya samu sama da kashi 68 cikin 100, kamar yadda shugaban hukumar zabe Badru Kiggundu ya sanar.Kizza Besigye ya zo na biyu a zaben da kashi 26 cikin 100, abinda ya baiwa Museveni Karin shekaru biyar bisa karagar mulki, bayan ya kwashe shekaru 25 kan madafun iko.Mai sa ido daga kungiyar kasashe renon England, Odein Bli Milla, ta koka kan hana 'yan adawa damar gogayya.