Tunisiya

An nada sabon Praminista a kasar Tunisiya

Sabon Praministan Tunisiya Beji Caid Essebsi
Sabon Praministan Tunisiya Beji Caid Essebsi AFP/Belaid

Hukomomin Kasar Tunisiya, sun nada Beji Caid Essebsi, a matsayin sabon Praministan kasar.Shi ne kuma zai maye gurbin Mohammed Ghannouchi, wanda ya yi murabus jiya.Wanan kuma bayan bukatar masu zanga-zanga, da ke neman ganin an karkade na kusa da Tsohon shugaban kasar, Zine El Abidine Ben Ali, daga mukaman Gwamnati.