Masar

Masar na kan hanyar shirya zabe da gyaren tsarin mulkin kasar

Tutar kasar Masar
Tutar kasar Masar DR

Mahukuntan mulkin sojan kasar Masar sun amince da gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulki a ranar 19 ga wannan wata na Maris.Bisa tsarin, za a gudanar da zaben majalisar dokoki a watan Yuni, bayan makonni shida, a yi zaben shugaban kasa.Daya daga cikin ‘yan kungiyoyi matasa da suka gudanar da taro da majalisar soja mai mulkin kasar ta Masar, ya tabbatar da amincewa da wannan tsari.