Zimbabwe

Zimbabwe kiran zanga-zangar nuna kyamar Mugabe

Morgan Tvangirai da  Robert Mugabe
Morgan Tvangirai da Robert Mugabe Montage RFI

An ci gaba da kiranye-kiranyen gudanar da zanga- zanga kan mulkin shekaru 31 na Robert Mugabe a kasar Zimbabwe. Wanan kuma duk da alwashin da jami’an tsaro su ka yi na dakushe kaifin ‘yan adawa.Mahukuntan kasar sun bayyana shirin dakile duk wani yunkurin kawar da gwamnati ta zanga- zanga salo irin na Tunisia, Masar da kuma abun da ke faruwa yanzu haka a kasar Libya.