Al'amura na kara rikicewa a kasar Libya
Wallafawa ranar:
Wani katon jirgin ruwa da aka shake shi da abinci don kaiwa mutanen yankin Benghazi dake gabashin kasar Libya, ya yi kwana ba shiri, ba tare da ya sauke kayan abincin ba.Bayanai daga Kungiyar Abinci ta duniya, mai helkwata a birnin Rome na kasar Italiya, na nuna cewa luguden wuta da akeyi a yankin ya hana jirgin isa inda aka tsara zai sauke kayan.Dan Shugaban kasar Libya Moamer Gaddafi, Seif Al-Islam ya ce ruwan bama-bamai da akeyi kan masu zanga-zanga ba don kasha su bane, saboda kawai a razana jama’a ne.Seif Al-Islam ya fadawa wata tashan TV dake Birtaniya, mai suna Sky News cewa, ‘yan tsagera na neman kwace iko ne, a wannan yanki na Brega, yasa akayi masu luguden.Ya ce allabaran baa da nufin kai harin kan fararen hula.Jakadan kasar Libya dake Amirka yace ‘yan adawa zasu hadu domin yin kafar ungula ga tsarin Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez dake wani tsarin sulhu gameda rikicin kasar Libya.Bayanai na cewa Jakadan Ali Aujali wanda yake sahun gaba wajen dawowa daga rakiyar Shugabansu Gaddafi, ya furta cewa sam ba zasu amince da wani sulhu ba.Wasu Wakilan majalisar Dattawan kasar Amirka sun bukaci sabuwar Gwamnatin da ake saran zata karbe iko daga hannun Shugaba Moammer Gaddafi data ga lallai an sake kama mutumin nan da ake zargi da harin jirgin sama na Lockerbie, a shekara ta 1988 inda mutane 270 suka mutu.Shidai mutun da ake zargin Abdel-Baset Ali Mahmet Al-Magrahi, dan shekaru 58, Hukumomin kasar Scotland sun sakeshi daga gidan kaso saboda ana ganin yana fama da cutar da bazai dade ba a duniya.