Masar

An kafa sabuwar gwamnatin kasar Masar

Le maréchal Mohamed Hussein Tantaoui shugaban majalisar soja mai mulkin kasar Masar
Le maréchal Mohamed Hussein Tantaoui shugaban majalisar soja mai mulkin kasar Masar Reuters/Goran Tomasevic/Files

An rantsar da ministocin sabuwar gwamnatin kasar Masar yau Litinin, a Alkahira babban birnin kasar.Shugaban majalisar soja mai mulkin kasar, Hussein Tantawi ya jagoranci gagarumin bikin, bayan juyin juya hali na zanga zanga cikin ruwan sanyi da ya yi awun gaba da tsohon shugaba Hosni Mubarak. Sabuwar gwamnatin kasar ta Masar karkashin Prime Minista Essam Sharaf ta kunshi sabbin ministoci guda shida.