Libya

Kasar Libya na fuskantar gagarumin rikici

Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, shugaban Libya Muamar Ghadafi ya amince, ta tura jami’an jinkai, akarkashin Tsohon Ministan harkokin wajen Jordan, Abdullah al Khatib.Rahotanni Daga kasar Libya, na nuna cewar, ana ci gaba da fafatawa tsakanin 'yan Tawaye dake dauke da makamai, da kuma dakarun dake gyoan bayan shugaba Muammar Ghadafi.Yan Tawayen sun ce, sun kwace Zawiyah, dake Yammacin Tripoli, yayin da dakarun Gwamnati suka kutsa cikin Misrata, suna anfani da manyan makamai, yayin da Gwamnati ke zargi Yan Tawayen da garkuwa da mutane, inji Khali Al qaem, kakakin ma’aikatar harkokin waje.Rikicin kasar ta Libya ya fara nuna alamun daukan lokaci fiye da yadda mahukuntan kasar suka dauka, kamar yadda masu nazarin lamura suka bayyana. Akwai kiyasi na dubban mutanen suka hallaka, da kuma wadanda suka samu raunika, sanadiyar yakin da ya barke a kasar ta Libya.