Sudan

Kusan mutane 60 sun hallaka a rikicin yankin Kudancin Sudan

Akalla mutane 56 sun hallaka sanadiyar karwa tsakanin dakarun kudancin Sudan da tsageru masu dauke da makamai.Lamarun ya faru kusa da Jihar Nile Upper mai arzikin mai, kamar yadda rindinar sojan kudancin Sudan ta bayyana. kakakin SPLM ya bayyana cewa kisan da akayi wa sojoji biyu ya janyo suka mayar da martani, inda aka hallaka tsageru 57, yayin da wasu sojojin bakwai suka rasa ransu.Tunda fari shugaban 'yan tawayen kudancin Sudan, Janar Athor George, ya yi tayin tsagaita wuta, bayan an kwashe makwanni biyu ana fafatawa tsakanin dakarunsa, da na gwamnati, abinda ya haifar da mutuwar mutane da dama.Janar Athor ya tabbatar da gwabzawar da akayi tsakanin dakarun sa da na gwamnati a karshen mako. 

Reuters/Yonhap