Libya

Rikicin kasar Libya ya Kazance

Majalisar Dinkin Duniya zata tura tawagar jami’an jinkai, dan ganewa idansu halin da ake ciki a kasar Libya.Ofishin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce zuwa yanzu fararen hula a cikin Libya, na cikin mawuyacin hali, a sassan da ake fafatawa tsakanin dakarun shugaba Muammar Ghadafi, da kuma 'yan tawayen dake dauke da makamai.Majalisar ta sanar da nada Abdelilah al Khatib, a matsayin jakada na musamman, wanda zai tattauana da jami’an Gwamnatin kasar Libya, dan kai agaji ga wadanda suka jikkata.Ban yace Ministan harkokin wajen Libya, Moussa Kusa, ya maince ya karbi jami’an jinkan da za’a tura kasar, cikin gaggawa, yayin da yayi kiran kawo karshen yadda ake cigaba da anfani da karfi kan fararen hula.Babbar jami’ar kul ada jinkai ta Majalisar, Valeri Amos, ta ce duk wadanda aka samu da laifin cin zarafin jama’a zasu fuskanci hukunci. Yan tawayen sun ce, sun kwace Zawiyah, dake yammacin Tripoli babban birnin kasar, yayin da dakarun gwamnati suka kutsa cikin garin Misrata, suna anfani da manyan makamai, yayin da gwamnati ke zargi 'yan tawayen da garkuwa da mutane, inji Khali Al qaem, kakakin ma’aikatar harkokin waje.Akwai dubban mutane da suka hallaka, da wasu da suka samu raunika a rikicin kasar kasar ta Libya dake yankin Arewacin Afrika, kamar yadda rohotanni suka tabbatar. 

Reuters