Angola

Sojojin kasar Angola na sintirin dakile bore

Birnin Luanda na Angola
Birnin Luanda na Angola RFI/Nicolas Champeaux

Yanzu haka sojojin kasar Angola na sintiri a Luanda babban birnin kasar, domin dakile wata zanga zanga da aka kira yau, domin adawa da ci gaba da shugabancin shugaba Jose Eduardo dos Santos, wanda ya kwashe shekaru 31 kan karagar mulki.Tun dai watan jiya ne, ake ta rade radin gudanar da zanga zangar, irin wanda ke faruwa a kasashen Arewacin Afrika, yayin da gwamnati ta ce, zata murkushe duk wata zanga zangar da ta taso.