Libya

Ana ci gaba da ruwan wuta a kasar Libya

Garin Ras Lanouf na kasar Libya
Garin Ras Lanouf na kasar Libya Reuters/Asmaa Waguih

An ci gaba da jin karar habe harbe a kan iyakan garin Ras Lanuf, da ‘yan tawayen kasar Libya ke rike da shi a yau Talata. An kuma ga ‘yan tawayen da dama suna tafiya a cikin manya da kananan motoci, yayin da wasu kuma ke takawa da kafa. Kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP, ya bayyana cewa an tsinkayo ‘yan tawaye uku da aka kai su wani asibiti dauke da munanan raunuka.Yan tawayen sun bayyana cewa sojan gwamnati sun musu luguden wuta a wannan yankin.A yau Talata ake sa ran, biyu daga cikin shugabannin ‘yan tawayen kasar Libya za su yi jawabi a gadan ‘yan majalisar dokokin kasashen turai ta EU. Shugaban ‘yan jama’iyyar Liberal a majalisar, Guy Verhofstadt yace tsohon ministan tsare tsaren kasar libya, Mahmud Jebril da tsohon jakadan kasar a India Ali Al-Isawi za su je birnin Strasbourg, don ganawa da ‘yan majalisar.A yau talata, Ma’aikatar harkokin wajenkasar Italiya ta ce za ta yi amfani da jiragen sama biyu don kwashe ‘yan kasar Bangladesh kusan 600, da suka yi gudun hijira zuwa kasar Tunisia sakamakon rikicin da ake yi a kasar ta Libya. Ma’aikatar harkokin wajen ta Italiya ta ce, wannan matakin dai na a matsayin wani kokarin ganin an shawo kan matsalolin da ke tasowa, sakamkon tumbatsar ‘yan gudun hijiran da suka gudu zuwa kan iyakar kasar ta Libya da Tunisiya, da suka kai kimanin dubu 25, kuma dubu 14 daga cikinsu ‘yan asalin kasar Bangladesh ne.Rahotanni sun bayyana cewa mai shiga tsakani na shugaban kasar Libya Mu’ammar Gaddafi ya yi tayin sasantawa tsakanin shugaban da ‘yan tawaye masu fada gwamnatin kasar kasar.Sai dai kuma a yau Talata, wani mai magana da yawun ‘yan tawayen ya sa kafa ya yi fatali da wannan tayin, inda ya ce su abin da suke so shine gaddafi ya fice daga kasar.