Cote d’ivoire

Laurent Gbago na Cote d'Ivoire ya kafa wata dokar fitar da cocoa

Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Laurent Gbagbo, ya kafa wata dokar da gwamnati kawai zata saya da kuma fitar da cocoa zuwa kasashen waje, domin dakile karfin mutumin da duniya ta amince da shi a matsayin zababben shugaban Alassane Ouatta.Dokar da aka karanta ta kafar talabijin ta kasar ta ce, daga yanzu babu wani dake da yanci saya da kuma fitar da cocoan zuwa kasuwannin duniya, sai Gwamnatin sa.Rohotanni daga kasar ta Cote d’Ivoire, na nuna cewar, mutanen garin Toulepleu, wanda ya fada hannun magoya bayan Allasane Ouattara, na ta barin garin, saboda kaucewa kai hari daga dakarun shugaba Laurent Gbagbo.Bayanna dake zuwa na nuna cewar, yanzu haka wasu mutanen garin, sun kafa tantuna a daji, su da iyalansu. 

Yan gudun hijirar kasar Cote d'Ivoire
Yan gudun hijirar kasar Cote d'Ivoire RFI/Claude Verlon