Libya

Rikicin kasar Libya ya haifar da dubban 'yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla mutane milyan daya ne ke bukatar agajin gagagwa a cikin kasar Libya, wadanda rikici ya ritsa da su kamar yadda babbar jami’a, Valeri Amos ta bayyana.Elizabeth Byers, kakakin hukumar agajin, ta yi bayani kan lokacin da ake saran jami’an ta zasu shiga kasar ta Libya, wadanda ke jiran amincewa.Bakin haure 'yan kasashen Afrika 1,000 suka isa Tsibirin Lampedusa, dake kasar Italiya, dan kaucewa tashin hankalin da ake fama da shi a kasashen Tunisia da Libya.Tuni kasar Italiya ta nemi taimakon kasashen Turai, dan magance yadda dubban bakin haure ke isa kasar.Tuni kasashen Faransa da Britaniya, suka bayyana shirin kokarin samun goyan bayan kwamiti Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a cikin wanna makon, domin hana jiragen sama zirga zirga a kasar Libya, domin karya karfi shugaba Muammar Gaddafi, wanda ke ci gaba da kai hari kan garuruwa masu adawa da shi.Wani jami’in diplomasiya ya shaidawa kanfanin Dillancin labaran Faransa cewa, tuni an kammala rubuda daftarin, saura kawai majalisar ta amince da shi.Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya ce kungiyar Tsaro ta NATO-OTAN, na nazarin yiwuwar anfani da karfin soji, dan magance rikicin kasar Libya.Amma anata bangaren Rasha ta ce bata goyan bayan duk wani yunkurin anfani da soji, dan magance rikicin siyasar kasar Libya.Ministan harkokin wajen kasar, Sergei Lavrov ya bayyana haka, inda yake cewa su basu amince da cewa ta anfani da soja ne za’a maganace matsalar ba. 

Bata ta kashi a garin  Ras Lanouf na kasar Libya
Bata ta kashi a garin Ras Lanouf na kasar Libya REUTERS/Goran Tomasevic