Libiya

Jini na ci gaba da kwarara kasa a kasar Libiya

Rikicin kasar Libiya,soji na cikin daga
Rikicin kasar Libiya,soji na cikin daga

Majalasar gudanar ta mulkin wucin gadi da Yan Tawayen Libya suka kafa, ta ki amincewa da tayin tattauanawa da shugaba Muammar Ghadafi yayi mata.Kakakin Majalisar, Mustapha Gheriani, ya bayyana bukatar su.In day a ke cewa:“Ba zamu tattaunawa ba da mutumin da yayi kisan kare dangi akan mutanen kasar mu ba, matsayin mu shi ne ba zamu tattauna ba, Ghaddafi ya zubar da jinni sosai, kuma ko da ya bar kasar nan, zamu bishi danganin ya fuskanci shari’a.”