Cote d’ivoire
Rikici na ci gaba da gudana a Cote-D’Ivoire
Wallafawa ranar:
A kalla mutane hudu ne aka kashe, a cigaba da tashin hankalin da ake fama da shi a kasar Cote- D’Ivoire.Wanan abu na cigaba da kunna wutar yakin basasaa a cikin kasar, a yayin da shugaba Laurent Gbagbo ya ki amincewa da ya halarci taron komitin tsaro da zaman lahiya na kungiyar tarrayar Afrika.Taron da zai gudanan ranar Alhamis 10 ga watan Maris a garin Addis –Abbeba na kasar HabashaBayanai na nuna cewar, akwai wasu kasashen dake baiwa shugaba Laurent Gbagbo goyan baya, kamar yadda Dr Mansur Idris na Jami’ar Bayero ya shaida mana.Kasashen da ake gani su 7 ne,daga cikin su a koye Angola,Afrika ta Kudu da kuma Ghana.