France-Libya

Dangantakar hulda ta kullu : tsakanin ‘yan tawayen Libiya da kasar France.

Tutar sabuwar Libiya a duniya
Tutar sabuwar Libiya a duniya Photo : Donaig Le Du et Manu Pochez

Shugaba Nicolas Sarkozy ya amunce da mambobin komitin rokon kwarya na kasar Libiya, komitin da ya kumshi ‘yan tawaye zalla, a matsayin masu wakiltar al’ummar kasar Libiya. Nan da lokaci kalilan ne ,kasar France za ta aika jakadan ta a garin Benghazi cibiyar yan tawayen.Ali Essaoui,wani manzo da rukunin ‘yan tawayen, shi ne sanar da aka a lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida.Tuni dai fadar shugaba Nicolas Sarkozy, ta tabatar da wanan magana kan aika jakada a Benghazi.Haka ma maganar ako da jakadu tsakanin Paris da Benghazi ta kassance tabatatar maganar da fadar shugaban kasar ta nanata.Mahmoud Jibril shi ma manzo daga bangaren ‘yan tawayen ya sanar da cewa, daga bakin gobe,kasar France za ta aje wani daftari a gaban kungiyar tarrayar turai ,daftarin da zai bada dama wajen hida ‘yan kasar Libiya , daga kangin wakalar da su ka shiga ciki.Sarkozy ya kassance shugaba na farko da ga cikin shugabanin kasashe 27 na tarrayar turai da ya karbi ‘yan tawayen kasar Libiya da hanu biyu,kuma ba tare da wata tantama ba.