Libiya

A Libiya fada na ci gaba da yin kamari

Mayakan sa kai a Libiya
Mayakan sa kai a Libiya

Yan tawayen kasar Libiya, da ke garin Benghazi, sun ce : zuwa yanzu, mutane 400 aka kashe a cikin gabashin kasar, tun bayan fara zanga-zangar adawa da shugaba Mumamar Ghaddafi.Wasu mutanan sama da 2,000 sun samu raunuka.Salah Jabar, wani jami’in kula da lafiya, ya ce wanan adadin ya fito daga garuruwan Derna, Baida, Brega, Benghazi, Ras Lanuf da kuma Bin Jawad.