Cote d’Ivoire

Alassane Ouattara da duniya ta dauka shugaban Cote d'Ivoire yana hanyar zuwa Najeriya

Alassane Ouattara da duniya ta tabbatar ya lashen zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire
Alassane Ouattara da duniya ta tabbatar ya lashen zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire AFP PHOTO/ SIMON MAINA

Kungiyar tarrayar Afrika ta kara jadada zaben Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasar Cote-D’Ivoire, sai dai yan bangaren Laurent Gbagabo, sun yi fatali da wannan tare da furta cewa: wannan makataki zai kara tsunduma kasar a cikin yakin basasa.Ouattara wanda ya halarci taron kan rikicin siyasar kasar ta Cote d'Ivoire da kungiyar Tarayyar Afrika ta kira, yanzu haka yana kan hanyar kai ziyara zuwa tarayyar Najeriya, domin ganawa da shugaba Goodluck Jonathan.Jonathan ke shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen AFrika ta Yamma, ECOWAS ko CEDEOA, wadda ta tsaya kai da fata, na ganin an tabbatar da rantsar da Ouattara bayan lashe zaben shekarar data gabata ta 2010.Prime Ministan kasar Kenya Raila Odinga ya nemi anfani da karfi domin kawo karshen ci gaa da rike madafun iko da Laurent Gbagbo ke yi a kasar ta Cote d'Ivoire dake yankin yammacin Afrika.