Nijar

Ana shirin gudanar da zaben shugaban Janhuriyar Nijar

Les campagnes officielles des candidats pour le deuxième tour de la présidentielle au Niger.
Les campagnes officielles des candidats pour le deuxième tour de la présidentielle au Niger. AFP/RFI

An rufe yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a gudanar gobe Asabar a kasar Janhuriyar Nijar. Ana fafatawa tsakanin 'yan takara biyu dake neman shugabancin kasar Mahamadou Issoufou daga jam’iyyar PNDS-Tarraya wanda ya yi na daya yayin zagayen farko, inda zai fafata da Seini Oumarou daga jam’iyyar MNSD-Nassara.Akwai masu zabe kimanin milyan 6.7, a kasar ta Janhuriyar Nijar dake yankin yammacin Afrika. Seini Omar tsohon Prime Ministan ya yi alkawrin ci gaba da aiyukan hambararren shugaba Mohammadu Tandja, yayin da Mahamadu Issoufou madugun 'yan adawa ya yi alkawarin kawo sauye sauyen ciyar da kasar gaba.Zaben shi ne matakin karshe na mayar da Janhuriyar Nijar bisa tafarkin demokaradiya, bayan juyin mulkin ranar 18 ga watan Febrairun shekara ta 2010, da aka kifar da gwamnatin Tandka, yayin da ya yi yunkurin tazarce bayana karewan wa'adin mulkinsa na shekaru 10.