Libya

Kasashen Faransa da Birtaniya na neman daukan mataki kan rikicin Libya

Ras Lanuf
Ras Lanuf REUTERS/Asmaa Waguih

Faransa ta nemi kungiyar kasashen tarayyar Turai ta amince da majalisar ‘yan adawan kasar Libya, yayin da ake shirin taron kungiyar.Wannan daidai lokacin da dakarun dake biyayya wa shugaba Muammar Gaddafi ke ci gaba kaddamar da hare hare kan ‘yan adawa.Kasashen Faransa da Birtaniya na neman daukan mataki kan shugaban Libya Gaddafi, muddun ya yi anfani da sinarai masu guba aakan al’umar kasarsa.Yanzu haka yakain kasar ta Libya ya zafafa musamman a garin Ras Lanuf mai tashan mai. Tuni dakarun Gaddafi ke bayyana samun nasara.Rikicin kasar ta Lbya ya yi kusan durkusar da man fetur da kasar ke fitarwa zuwa kasashen duniya, wanda ke samar mata da kudaden musaya. Yanzu kasar tana fitar da gangunan mai dubu-dari-biyu (200,000) zuwa dubu-dari-uku (300,000) maimakon ganguna milyan 1.4 da kasar ke fitarwa kafin rikice lamura.