Cote d’Ivoire

Kungiyar kasashen Afrika ta nuna goyon bayan Ouattara

Kungiyar tarayyar Afrika ta bayyana amincewarta da Alassane Ouattara a matsayin cikakken shugaban kasar Cote d'Ivoire, bayan jerangiyar da ta sha wajen shawo kan Laurent Gbagbo ya yarda ya mika jan ragamar mulkin kasar ga Ouattara, amma yaki.Shugaban kasar ta Cote d'Ivoire da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar Alassane Ouattara da marecen yau Juma’a ne, zai sauka a birnin Abujan tarayyar Nigeriya, inda zai gana da shugaban kasar Goodluck Jonathan,A firar da ya yi a safiyar yau Juma’a a birnin Adis Ababa da PM kasar Habasha Meles Zanawi, Ouattara ya bayyana cewa, zai je birnin na Abuja domin tattunawa ta tsawon 'yan kwanaki da shugaba Jonathan kan rikicin siyasar kasarsa Cote d'Ivoire, kafin ya zarce zuwa birnin Abidjan a wani lokaci da ba a ambata ba, saboda dalilan tsaro.

Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire
Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire Reuters/Thierry Gouegnon