Najeriya

Shugaban Najeriya Jonathan ya gana da sauran 'yan takara

Shugaban kasar Nigeriya Goodluck Jonathan ya yi wata ganawa yau Jumma'a da daukacin 'yan takaran shugabancin kasar na wata mai zuwa, dangane da kokarin ganin an gudanar da lamuran zaben cikin tsanaki da kwanciyar hankali. A lokacin ganawar tasu shugaba Jonathan ya sake nanata masu burinsa na ganin ya gudanar da tsarkakkaken zabe a wannan wargajejiyar kasa ta fuskar jama’a a nahiyar Afrika.Ya kuma nuna fargabarsa kan yadda kafin zuwan zaben ake ci gaba da sumu tashe tashen hankula nan da can a ko ina cikin fadin kasar, inda ya ce gaba dayansu 'yan takarar ya san babu wanda za iso kasar ta fada cikin mawucin hali.