Nijar
Shugaban sojan Nijar ya gana da 'yan takara
Shugaban kasar Janhuriyar Niger Janar Salou Djibo ya yi wata ganawa da yan takarar shugabancin kasar biyu Seini Omar na jama’iyar MNSD Nasara da Mahamadou Issoufu na jam’iyar PNDS Tarayya tare da shugaban hukumar zaben kasar CENI Abdurahaman Gusman, a daidai lokacin da a gobe Asabar za a je zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar.Gwamnatin mulkin sojan ta nemi 'yan siyasan da su nuna hali na gari, tare da runguman kaddara duk wanda ya lashe zaben na shugaban kasa. Janar Djibo ya bayyana cewa ci gabar kasar shi ne abu mahimmi ba tashin hankali ba.
Wallafawa ranar: