Libya

Taron kasashen Turai kan rikicin Libya

Shugaban Jamus Merkel dana Faransa Sarkozy a wajen taron Turai kan rikicin Libya
Shugaban Jamus Merkel dana Faransa Sarkozy a wajen taron Turai kan rikicin Libya REUTERS

A yau juma’a mahukumtan tarayyar Turai sun ci gaba da kokarin goge banbance banbancen dake tsakaninsu dangane da kasar Libiya, a wani taron dinke baraka, mahukumtan Paris da Landon na ta kokarin ganin an matsa kaimi wajen daukar matakan soja kan gwamnatin Gaddafi, tare da amincewa da 'yan tawayen kasarKasar Luxembourg dai ta nuna adawarta karara, bisa yadda Faransa ta yi gaban kanta wajen amincewa da 'yan tawayen kasar ta Libiya, ba tare da jin ra’ayi sauran kasashen Turai ba.A lokacin da yake mayar da martani shugaba Gadafi ya yi kashedi ga kasashen Turai, dangane da goyon bayan da suke baiwa 'yan tawayen, da cewa zai tsame hannayensa, daga hana bakin haure kutsa kai a nahiyar ta Turai.Yan tawayen kasar ta Libiya sun kara tura dakaru a garin nan mai arzikin man Petur na Ras Lanouf, dake yankin gabashin kasar, inda dakarun gwamnatin shugaba Gaddafi suka koresu a jiya Alhamis.Rahotannin sun bayyana cewa, ana ci gaba da bata kashi tsakanin yan tsageran da dakarun da ke biyayya ga gwamnatin Gaddafi, inda a halin yanzu mawuyacin abu ne, a iya tantance yadda lamuran ke kasancewa a can, kamar yadda yan jaridu suka tabbatar.