Libya

Manyan kasashen duniya sun nemi shugaban Libya Gaddafi ya ajiye aiki

Manuel Pochez/ RFI

Kungiyar kasashen tarayyar Turai da kasar Amurka sun bukaci shugaban Libya Muammar Gaddafi dake fuskan bore, da yayi murabus.Bayan taron da kungiyar ta gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium, shugabannin kasashen na Turai sun amince da daukan matakan kare fararen hular Libya, yayin da shugabna kasar Amurka Barack Obama ya bayyana cewa kasar zata daukan matakan tabbatar da cewa Gaddafi ya yi ban kwana da madafun iko.Wannan daidai lokacin da rikcin kasar ta Libya ke rincabewa, inda dakarun dake biyayya wa Gaddafi ke anfani da jiragen saman yaki wajen kai hare hare cikin yankunan masu adawa.Dubban ‘yan gudun hijira sun tsare, yayin da kasar Afrika ta Kudu ta rufe asusun ajiyan Gaddafi.