Cote d’Ivoire

Ouattara ya isa tarayyar Najeriya

Alassane Ouattara
Alassane Ouattara France 24

Mutumin da kasashen duniya suka hakikance ya lashe zaben shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya fara ziyara ta wkanaki, a Abuja babban birnin tarayyar Nigeria.Wannan a ci gaba da neman matsin lamaba wa Laurent Gbagbo ya yi ban kwana da madafun iko bayan faduwa a zaben watan Nowamba.Kwamitin Sulhun MDD ya yi maraba da matakin da tarayyar Afrika ta dauka na amince da cewa Ouattara shi ne halartattacen shugaban kasar Cote d’Ivoire tare da barazanar lankaya takunkumi wa duk wanda ya nemi wargi da zaman lafiyar kasar.Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta bayyana cewa fiye da mutane 450,000 suka tsare daga gidajensu sakamakon rikicin siyasar kasar.