Nijar

Ana jiran sakamkon zaben shugaban Janhuriyar Nija

Masu zaben Janhuriyar Nijar
Masu zaben Janhuriyar Nijar AFP/SEYLLOU

Ana ci gaba da zaman jiran samakaon zaben shugaban kasar Janhuriyar Nijar, wanda aka gudanar jiya Lahadi. Zaben shugaban kasar zagaye na biyu, zai tantance mutumin da zai jagoranci kasar na gaba, tsakanin Mahamadou Issoufou da tsohon PM Seini Oumarou.Masu sa ido a zaben shugaban Janhuriyar daga kungiyar kasashen tarayyar Turai, sun yaba da yadda zaben ya gudana, inda suka bukaci kasashen Afrika da suyi koyi da kasar.Jagoran tawagar, Santiago Fisas, ya bayyana zaben a matsayin nasara ga al’ummar kasar ta Janhuriyar Nijar.