Libya

Dakarun Libya sun sake kwato wani gari daga 'yan tawaye

Benghazi
Benghazi RFI/Manu Pochez

YAN Tawayen Libya, dake dauke da makamai sun kori dakarun shugaba Muammar Ghadafi daga garin Brefa, bayan fafatawar da sukayi.Rahotanni sun ce, an samu rasa rayuka a fadan da aka gwabza. A wani labarin dakarun dake biyayya wa Gaddafi sun bayyana sake kwato garin Brega, yayin da suke ci gaba da neman dannawa cikin yankunan da 'yan tawaye ke da karfi.Dubban mutane sun hallaka yayin da rikicin kasar ta Libya ke ci gaba da faruwa. Tuni kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana goyon bayan ganin an haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar ta Libya.Sakatariyar Harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, yau zata gana da 'yan tawayen Libya a birnin Paris, domin duba hanyar da zata taimaka musu yakar Gaddafi.Ana saran kuma zata gana da wakilan kasashen takwas da kuma kungiyar kasashen Larabawa domin samun nasarar aiwatar da hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar ta Libya.