Nijar

Janhuriyar Nijar ta samu sabon zababben shugaba

Mahamadou Issoufou sabon zababben shugaban kasar Janhuriyar Nijar
Mahamadou Issoufou sabon zababben shugaban kasar Janhuriyar Nijar AFP/ Boureima HAMA

Sakamakon zaben shugaban Janhuriyar Nijar ya tabbatar da nasara wa dadaddan dan Mahamadou Issoufou na jam’iyyar PNDS Tarayya da kashi 57.95 cikin 100 na kuri’un da aka kada baki daya.Zabebben shugaban Issoufou ya doke tsohon PM Seini Oumarou na jam’iyyar MNSD Nasara, kamar yadda hukumar zaben kasar ta aiyana yau Litinin.Issoufou dan shekaru 59 da haihuwa ya kayar da tshon PM Seini Oumarou dan shekaru 60 da haihuwa, wanda ya samu kashi 42 cikin 100 na kuri’un da aka kada.An samu fitowar masu zabe na kashi 48.17 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben kasar ta Janhuriyar Nijar ta aiyana, wato kasa da kashi 51.56 cikin 100, yayin zagaye na farko, a cewar shugaban hukumar zabe Abdourahamane Gousmane.Hukumar zaben ta ce mutane milyan 3.3 suka kada kuri’unsu, inda Mahammadou Issofou ya samu kuri’u milyan 1,820,639 yayin da Seini Oumarou ya samu kuri’u milyan 1,321,248.Ana rasan gwamnatin mulkin sojan kasar ta Janhuriyar Nijar, karkashin Janar Salou Djibo, ta mika mulki wa mutumin da ya lashe zaben Issoufou madafun iko, ranar shida ga watan gobe na Afrilu, kamar yadda aka tsara.Yanzu sakamakon zaben zai jira amincewar kotun tsarin mulki wadda ta ke da tacewa ta karshe kan amincewa da sakamakon.A shekarar 1960 kasar ta samu ‘yanci daga Turawan mulkin mallakan kasar Faransa, kuma kasar ta fuskanci juye juyen mulki daga sojoji.