Chadi

Shugaban Chadi Deby ya amince da dage zaben shugaban kasa

Idriss Deby shugaban kasar Chadi
Idriss Deby shugaban kasar Chadi AFP

Shugaban Kasar Chadi, Idris Deby, ya amince ya dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar uku ga watan gobe, sakamakon barazanar kauracewa zaben da 'yan adawa suka yi.Nadji Madou, daya daga cikin 'yan takaran ya ce, bayan ganawa da shugaban, ya amince dage zaben zuwa wani lokaci nan gaba.