Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Shugaban Kabila ya sallmi wasu ministoci

Shugaban kasar Janhuriyar demokradiyar Congo, Joseph Kabila, ya kori ministocin sa biyu, saboda abinda ya kira cin hanci da rashawa, da kuma kauracewa wurin aiki.Ministan yada labaran kasar, Lambert Mende, ya ce an kori mataimakin Prime Minista, Nzanga Mobuto, Dan marigayi shugaba Mobuto Sese Soko, saboda kwashe watanni uku a Turai, yayin da aka kori Philipe Undji, saboda zargin cin hanci. 

Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo (Photo: AFP)