Najeriya

Tsagerun yankin Nija Delta na Najeriya na barazana

Reuters

Kungiyar dake ikrarin Yantar da Yankin Niger Delta, ta tsagerun MEND mai dauke da makamai, ta yi alkawarin kaddamar da sabbin hare haren bama bamai a garuruwan Lagos da Abuja.Wata sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labarai, cikinsu harda Rediyon Faransa, kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da yaudara, wajen biyan bukatunsu, inda take baiwa wasu mutanen Yankin cin hanci, wajen yaudarar mutanen Niger Delta.Kungiyar ta ce, zata dinga bada sanarwar mintoci 30 kafin kai harin.