Libya
Dakarun dake biyayya wa Gaddafi na Libya sun bayyana samun galba
Dakarun dake biyayya ga shugaban kasar Libiya Ma’amar Kaddafi sun samu galaba a kasar, wata guda bayan barkewar zanga zangar kin jinin gwamnati da ta juya zuwa yakin basasa, a daya bangaren kuma kungiyar kasashe takwas masu karfin tattalin arzikin na duniya G8, basu cimma daidaito kan daukar matakan soja a kan kasar ta Libiya ba.A cikin wata hira da jaridar kasar Italiya Il Giornale shugaba Gaddafi ya bayyana cewa daga yanzu 'yan tawaye sun rasa nasara, tare da kin yin duk wata tattaunawa da su,Ministan harakokin wajen kasar Faransa Alain Juppe ya bayyana cewa zasu nemi MDD da ta kara matsa kaiminta kan shugaba Gaddafi.
Wallafawa ranar: