Libya

Dakarun dake goyon bayan Shugaba Gaddafi na Libya na ci gaba da ruwan wuta

Dakarun Shugaba Muammar Ghaddafi na kasar Libya, na ci gaba da aman wuta a garuruwan Ajdabya da Zuwara, wadanda ke kusa da Benghazi, yayin da kungiyar kasashen takwas da suka fi habakar masana’antu suka kasa samun goyan bayan anfani da karfi a Libya.Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce Ghadafi na kashe sojojin da suka ki kashe 'yan tawayen. Yanzu haka fada na kara zafi, yayin da dakarun Gaddafi ke ruwan wuta ta sama babu ji babu gani. Akwai wuraren da aka samu sabbin fafatawa tsakanin masu bore da masu goyon bayan Gaddafi.Yanzu kaha harkokin hakar man fetur na kasar sun durkushe baki daya, saboda mawuyacin halin da kasar ta samu kanta. 

REUTERS/Finbarr O'Reilly