Samaliya

Kotun Amurka ta dauke barayin gaban ruwan Somaliya

Reuters

Wata kotu a kasar Amurka, ta daure wasu 'yan fashin jiragen ruwan Somaliya biyar rai da rai, da kuma karin shekaru 80 a gidan yari, saboda harin da suka kaiwa jirgin ruwan Amurka.Alkalin kotun ya yi watsi da daukaka karar da wadanda ake zargin suka gabatar. Barayin gaban ruwan kasar ta Somaliya sun yi kaurin wajen garkuwa da jiragen ruwan kasashen duniya masu wucewa ta kaban tekun kasar, tare da neman kudaden fansa.