Cote d’Ivoire

Ouattara ya tsawaita takunkumin fitar da koko na Cote d'ivoire

Alassane Ouattara durante una conferencia de prensa, el 24 de diciembre.
Alassane Ouattara durante una conferencia de prensa, el 24 de diciembre. ©REUTERS/Stringer

Zababben Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara, ya tsawaita hana fitar da kokon kasar kasashen waje, zuwa karshen wannan watan, a yunkurin hana shugaba Laurent Gbagbgo samun kudaden shiga.Kasar tana ci gaba da fuskantar rikici tun bayan zaben watan Nowamba, wanda MDD ta tabbatar Ouattara ya lashe, amma Laurent Gbagbo ya ci gaba da rike madafun iko da taimakon rindinar sojan kasar ta Cote d'Ivoire. Ranar Litinin fada ya kaure cikin birnin na Abidjan a yankin dake karkashin ikon Gbagbo.Yanzu haka fada na zafafa a birnin na Abidjan dake zaman helkwatar Gbagbo da Ouattara. Tuni kasashen duniya suka saka takunkumi kan Gbagbo da 'yan kanzaginsa.