Nijar

Tarayyar Turai ta yaba da zaben Janhuriyar Nijar

Kungiyar tarayyar Turai ta yaba da zaben da aka yiwa shugaban yan adawar kasar Janhuriyar Niger Mahamadou Issoufou a kan karagar shugabancin kasar, tare da bayyana matakin da cewa, shine aiki mafi muhimmanci da gwamnatin rikon kwaryar Demokradiyar kasar ta yi, wanda hakan zai sake maida huldar kasar da kungiyar ta Tarayyar Turai.A nasa bangaren sabon shugaban kasar ta Janhuriyar Mahamadou Issoufou ya nemin shugaban kasar Cote d'Ivoire mai barin gado Laurent Gbagbo, da ya gaggwauta tattara nasa ya nasa ya mika mulki ga zababben shugaban kasar Alassane Ouattara.Tare da nuna takaicinsa dangane da halin da kasar ta Cote d'Ivoire ke ciki, sanadiyar son rai irin na Laurent Gbagbo.  

Mahamadou Issoufou zababben shugaban kasar Janhuriyar Nijar
Mahamadou Issoufou zababben shugaban kasar Janhuriyar Nijar Voice of America