Janhuriyar Tsakiyar Afrika

Yan tawayen Uganda sun kai hari Afrika ta Tsakiya

Akalla mutane shida ne aka kashe yayinda aka yi awon gaba da wasu sama da 30 a cikin wani hari da 'yan tawayen l’Armee de Resistance du Seineur (LRA) suka kai masu a yankin Nzako a yankin tsakiya maso gabashin kasar Janhuriyar Tsakkiyar Afrika, kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar.Wata majiyar mai tushe ta bayyana cewa daga cikin mutanen 6 da aka kashe sun hada ne da sojoji hudu tare da sace mutane 30-50 kamar yadda majiyar sojojin Bakuma mai tazarar kilo mita 60 da yankin Nzako da lamarin ya faru ta sanar. 

AFP/Lionel Healing