Nijar

Zababben shugaban Janhuriyar Nijar Issoufou ya nemi hadin kan 'yan kasa

Zababben shugaban Janhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou
Zababben shugaban Janhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou AFP / BOUREIMA HAMA

Zababben Shugaban kasar Janhuriyar Nijar, Muhamadou Issoufou, ya bayyana farin cikin sa da nasarar da ya samu, a zaben da akayi a karshen mako.Shidai Mahamaduo Issoufou dan shekaru 59 a duniya, ya fito ne daga kabilar Hausa mafi rinjaye a kasar ta Janhuriyar Nijar, ya kuma fito ne daga Jihar Tawa dake yankin yammacin kasar, injiniya ne ta fuskar Ma’adanai, kafin ya zama ma’aikaci a karkashin katafaren kamfanin samar da makamshin Nukliyar kasar Faransa Areva, wanda ke hakar karfen Uraniyom din kasar ta Nijar.Sai dai kuma ya sadaukar da rayuwarsa kan shi’anin siyasa shekaru kusan 20 da suka gabata, inda daga shekarar 1993-1994 ya zama PM kasar a karkashin Mulkin Maman Usman, kafin su raba gari ya zama shugaban Majalisar Dokokin kasar daga 1995 zuwa 1996.Ya sha kaye a zaben shugabancin kasar na Shekarar 1999 da kuma na 2004 daga hannun Tandja Mamadou,Mahamadu Issoufou mai lakabin Sunan Zaki, mai matsakaicin Tsawo da Farar Fata, daga shekara ta 2009 ya yi gwagwarmayar siyasar hanawa shugaba Tanja Mamadu zarcewa kan Mulkin kasar, bayan cikar wa’adinsa na shekaru 10 ba kari, inda daga bisani Sojoji suka raba gardamar ta hanyar juyin mulki.Ma’auracine mijin Mace 2 da yaya 4, Mahamadu- Zaki wanda ya kasance Musulmi ya soma jin kanshin Nasarar samun Mulkin kasar ta Niger ne dake fama da matsalolin Tattalin Arziki, tun a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a 11 ga watan janairun da ya kabata, inda jam’iyarsa ta PNDS Tarayya ta samu gagarumar nasara. Kafin wanan lokaci da hukumar zaben kasar CENI ta ayyana shi a Matsayin wanda ya lashe zaben.