Najeriya

Hadin kan Jam’iyyu don kada PDP a zaben watan Aprilu

'Yan takarar shugaban kasar Nijeriya na Jam'iyyun adawa. Gen. Buhari da Ribadu da shekarau da Pat Utomi
'Yan takarar shugaban kasar Nijeriya na Jam'iyyun adawa. Gen. Buhari da Ribadu da shekarau da Pat Utomi

Kayar da jam’iyyar PDP mai mulki a zabe mai zuwa shi ne dai babban kalubalen da ke gaban Jam’iyyun adawa a Najeriya, sai dai kuma masu sharhi kan lamurran siyasa a kasar suna ganin canza sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wata jam’iyyar wata manuniya ce ta rashin akida tsakanin jam’iyyun tare da rashin sa kishin kasa a gabansu.Tuni dai jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa zata mulkin Najeriya a shekaru sittin masu zuwa bayan kwashe shekaru goma tana mulki tun da kasar ta dawo mulkin demokradiya daga mulkin soji a shekarar 1999.Da dadewa ne dai wasu jam’iyyun adawa a kasar suke neman kulla kawance don tunkarar jam’iyyar PDP a zaben watan Aprilun bana amma har yanzu kawance ya ci tura misali kawancen da jam’iyyar CPC ta madugun adawa Gen Muhammadu Buhari ta so kullawa da jam’iyyar ACN wacce ta mamaye yankin kudu masu yammacin kasar. 

Talla

A yanzu haka dai jam’iyyar ANPP wacce ta dade tana hamayya da PDP tace har yanzu akwai fatar hadin kan jam’iyyun don kalubalantar jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa kamar yadda Alh. Shettima Lawan, sakataren Jam’iyyar na kasa yace har yanzu akwai tattaunawa da ke gudana tsakanin ‘yan takarar jam’iyyu musamman tsakanin dan takarar Jam’iyyar CPC Gen. Muhammadu Buhari da Nuhu Ribadu na jam’iyyar ACN da Mallam Ibrahim Shekarau na ANPP da kuma Pat Otumi.

Alh. Shettima Lawan Sakataren Jam'iyyar ANPP na kasa

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI