Cote d’Ivoire

Mutane 30 sun mutu a wani harin da magoya bayan Gbagbo suka kai

hayakin hare haren da magoya bayan Gbagbo suka kai a Abobo Abidjan Babban birnin kasar
hayakin hare haren da magoya bayan Gbagbo suka kai a Abobo Abidjan Babban birnin kasar Reuters

Kimanin mutane 30 ne suka mutu, sanadiyar wani hari da dakarun dake biyayya ga Laurent Gbagbo suka kai a wata unguwar dake nuna goyon bayansu ga abokin hamayyarsa Alassane Ouattara wanda duniya ta amince da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.Al’amarin dai ya faru ne a wata babbar kasuwa dake a unguwar Abobo a Abidjan babban birnin kasar.Kakakin Majalisar Dunkin Duniya Hamadoun Toure ne ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis, inda aka kai harin kan magoya bayan Alassane Ouattara da duniya ke dauka zababben shugaban kasa.Kasar Cote d’Ivoire dai ta shiga cikin rikici tun bayan zaben watan Nuwamba da Gbagbo yaki amincewa da shan kaye a zaben, tare da ci gaba da kakumewa kan madafun ikon kasar.