Senegal

‘Yan adawa sun kudurta gudanar da zanga-zanga a Senegal

Shugaban kasar sénégalais Abdoulaye Wade
Shugaban kasar sénégalais Abdoulaye Wade AFP/Seyllou

Masu adawa da gwamnatin kasar Senegal sun bayyana shirya gudanar da zanga-zanga a gobe Assabar babban Dandalin da suka kira Tahrir a Dakar babban Birnin kasar.Jam’iyyun adawa ne a kasar suka hada wani kawance domin gudanar da zanga-zanga a ranar da shugaban kasar Abdoulaye Wade ke cika shekaru 11 a kan karagar mulkin kasar.Al’ummar kasar dai na adawa da gwamanatin Wade ne bisa halin tsadar rayuwa da ake fama a kasar da matsanancin matsalar wutar lantarki. Wani zargin kuma da ‘yan adawa ke wa shugaban shi ne na karya kundin tsarin mulkin kasar domin ba shi damar zarcewa kan karagar mulki wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Fabrairun shekarar 2012.Yunkurin gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasashen Africa da dama bai yi tasiri ba musamman kasashen Kamaru da Gabon da Angola da Zimbabwe da Togo da Mouritania inda jami’an tsaro suka yi Fatali da masu gudanar da zanga-zangar.