Masar

Ana zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin Masar

Masu zaben kasar Masar da suka kai milyan 45 ake saran zasu kada kuri’ar raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin kasar.Wannan ya zama kwajin demokaradiya na farko da kasar ke fuskanta, bayan kawo karshen mulkin Hosni Murabak na shekaru 30 ta hanyar zanga zangar lumana.Sabon kundin tsarin mulkin ya kaiyade wa’adin shugaban kasa, tare da kirkiro makamun mataimakin shugaban kasa.Manyan jam’iyyun kasar sun nemi masu zabe da su amince da sabon kundin tsarin mulkin, amma masu rajin kare hakkin bil Adam, ayi watsi da shi, saboda sauye sauye basu yi ba. 

Reuters/Amr Abdallah Dalsh