Cote d’Ivoire
Gbagbo na neman fararen hula su bashi hadin kai
Laurent Gbagbo dake ci gaba da karfa karfa kan madafun ikon kasar Cote d’Ivoire ya nemi fararen hula su taimaka wa dakarun kasar, domin kawar da wadanda ya kira ‘yan tawaye dake barazana wa birnin Abidjan.Wannan daidai lokacin da MDD ta bayyana cewa hare haren da dakarun dake biyayya wa Gbagbo ke kaiwa laifi kan bil Adam, abunda magoya bayansa suka musanta.Kasar ta Cote d’Ivoire dake yankin yammacin Afrika, ta fada cikin rikicin siyasa bayan zaben watan Nowamba da Alassane Ouattara ya lashe, amma Gbagbo yaki amincewa da shan kayi bayan mulkin shekaru 10, kuma ya na samu daurin kindin sojojin kasar, ko ya yake duniya ta juya masa baya.
Wallafawa ranar: