Hukumar zaben Najeriya ta kawar da yuwuwar sauya lokacin zabe
Wallafawa ranar:
Hukumar zaben tarayyar Nigeria mai zaman kanta ta yi watsi da bukatar ‘yan adawa na neman sauya lokacin gudanar da zaben shugaban kasa na watan gobe.Hukumar ta bayyana cewa lokaci ya kure ga duk wani gyara, ‘yan ada sun nemi bayar da zaben shugaban kasa ya zama na karshe.Bisa tsarin ranar 2 ga watan gobe na Afrilu za a gudanar da zaben ‘yan majalisun tarayya, majalisar wakilai data dattawa, yayin da ranar 9 ga wata a gudanar da na shugaban kasar, sannan ranar 16 a kammala da zaben gwamnanoni jihohin kasar 36 da ‘yan majalisun jihohin.Yan adawa na tsoron muddun shugaba Goodluck Jonathan ya lashe zabe, jam’iyyar PDP mai mulki zata samu gagarumin nasara, yayin sauran zabukan.