Libya

Kasashen Yammacin Duniya sun na Ruwan wuta wa dakarun Gaddafi na Libya

REUTERS/ECPAD/Sebastien Dupont

Manyan kasashen Faransa, Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare hare ta sama, domin karya lagon shugaban Libya Muammar Gaddafi, bisa neman tabbatar da aiki da kudirin Kwamitin Sulhun MDD da ya haramta shawagin jiragen sama, a sararin samaniyar kasar.Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce dakarun Amurka dana Birtaniya sun cilla makamai masu linzani 110, yayin da zaratan jiragen saman yakin Faransa suka farma dakarun dake goyon bayan Gaddafi masu kai hari birnin Benghazi.Shugaban Libya Muammar Gaddafi ya yi alkawarin daukan fansa tare da cewa zai bude rumbun makamai, domin raba wa al’umar kasar.Da karfi 4:45 na yammacin jiya Asabar agogon TU jiragen saman yakin Faransa suka kaddamar da hariShugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya bayyana cewa kasashen yammacin duniya dana Larabawa sun kaddamar da hari, domin haramta wa dakarun shugaban Libya Muammar Gaddafi ci gaba da kai hari wa hararen hular Benghazi.Ya bayyana haka a birnin Paris yayin taro da PM Birtaniya David Cameron, Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton da wasu shugabanni.PM Birtaniya Cameron ya tabbatar da cewa dakarun kasar sun shiga cikin kai farmakin.Shugaban AMurka Barack Obama ya ce kasar ta shiga saboda kare fararen hula bayan kalaman Gaddafi na kaddamar da farmaki babu tausayi.